Sabuwar fasahar dai zata kula da a kalla kashi ɗaya cikin ɗari na jimillar albashin kamfanin wanda yake da ma’aikata fiye da miliyan ɗaya a duniya
Haka kuma ta bayyana cewa kamfanin tsara rage ma’aikatan ne tun a ƙarshen watan jiya na Satumba.
Rahoton Jaridar ya ya kuma yi nuni da cewa wuraren da abin ya shafa za su kasance a cikin sashen na’urori na Amazon, sashin tallace-tallace da kuma na albarkatun ɗan adam.
Haka dai Rahoton ya ce, adadin ma’aikatan da aka kora na iya canjawa, amma idan har aka tabbatar da hakan, zai kasance zagayen korar mafi girma a tarihin kamfanin mai shekaru 28 da Jeff Bezos ya kafa.
A makonni biyu da suka gabata kamfanin Amazon ya ba da sanarwar dakatar da daukar ma’aikata kuma tuni ma’aikatan sa suka ragu idan aka kwatanta da tsarin a farkon shekara.
