Labarai
Hukumar EFCC Ta Kama Wani Dan Kasuwar Canjin Kudaden Ketare
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta kama wani da ake zargi da canji kudaden ketare ba bisa Ka’ida ba, Mustapha Muhammed wanda aka fi sani da Muaspaha Naira a Abuja.
EFCC ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Laraba sannan ta kuma fitar da hoton wanda ake zargin.
Hukumar ta ce an kama shi ne a wani yunkuri na hukumar na kawar da harkar canjin kudaden waje.
Ta ce an kama shi ne a ranar Asabar a unguwar Wuse da ke babban birnin tarayya Abuja.
Ta wallafa a shafinta na twitter cewa, “A ci gaba da gudanar da ayyukanta na kawar da harkar canjin kudaden waje da kuma kawar da masu tinanin aikata irin haka da duk wani nau’in zagon kasa ga tattalin arzikin kasa, EFCC ta kama wani Mustapha Muhammed da ake kira Mustapha Naira.
“Jami’an hukumar ne suka dauke shi a ranar Asabar, 12 ga watan Nuwambar 2022, a Wuse Zone 4, cibiyar hada-hadar kasuwanci a babban birnin tarayya.
“Wanda ake zargin ya yi bayani mai amfani yayin da ake ci gaba da bincike.”
