Labarai
Hukumar INEC Za Ta Fara Yada Labarai Na Mako-mako Gabanin Zaben 2023
Yayin da ya rage kwanaki 100 a gudanar da babban zaben shekarar 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta fara taron manema labarai na mako-mako don sanar da ‘yan Najeriya ci gaban da hukumar ta samu.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a ranar Larabar nan, Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu ya ce hukumar za ta fara ne da gabatar da bayanai na mako biyu sannan daga baya za ta ci gaba da gabatar da bayanai na mako-mako da na yau da kullun.
Shugaban na INEC ya nanata biyayyar hukumar ga ‘yan Najeriya da ke son gudanar da sahihin zabe ta hanya amfani da fasahar zamani, wanda ke ba da tabbacin tantancewa da kuma shigar da sakamakon rumfunan zabe ga ‘yan kasa su gani nan take a ranar zabe.
Ya kuma kara nanata cewa babu gudu babu ja da baya wajen amfani da na’urar Bimodal Voter Accreditation System (BVAS) da kuma dorawa a shafin INEC Result Viewing Portal (IReV) a babban zaben 2023.
Mahmood ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da shugabannin siyasa da su gudanar da yakin neman zabensu cikin lumana, tare da gujewa rarrabuwar kawuna, nuna kyama da tashin hankali.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa, A yayin da ya yi alkawarin ci gaba da bayar da gudunmuwarsu cikin himma da sanin ya kamata, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki, ‘yan kasar da su bayar da nasu gudunmuwar domin baiwa ‘yan Najeriya zabukan da suke so.
