Labarai
Muna Da Shirin Ko Ta Kwana Don Zuwa Zagaye Na 2 A Zaben 2023 – INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce tuni ta fara shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda babu wani dan takara da ya cika sharuddan lashe zabe a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Mista Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wani taro da shugabannin Ku.giyar Editocin yada labarai a ranar Juma’a a Abuja.
Okoye ya ce irin wannan tsari ya kasance al’adar INEC na duk zabukan da hukumar ta gudanar tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya tun 1999.
Ya ce tuni INEC ta shirya buga ninki biyu na adadin takardun zabe da ake bukata domin kada kuri’a na farko, idan har sai an sake zaben.
Ya bayyana cewa, shirye-shiryen su kadai ake yin su na farko domin hukumar na da kwanaki 21 kacal don gudanar da zaben ko kuma fidda gwanin da ya ci.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Kwamishinan na kasa ya ce kafin a ayyana dan takarar a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, dole ne ya samu mafi yawan kuri’un da aka kada sannan ya samu kashi biyu cikin uku na jihohin tarayya da na babban birnin tarayya Abuja.
Ya ce a inda wani dan takara bai samu nasara ba, kundin tsarin mulkin ya ce a gudanar da zabe na biyu na biyu daga cikin ‘yan takarar da ke da kuri’u mafi girma da rinjaye kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
“Sashe na 134 karamin sashe na 2 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, wanda shi ne tushen dokar kasa, ya wajabta kafin a ce an zabe wani a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya, dole ne dan takarar ya tabbatar da samun mafi yawan kuri’un da aka kada a zaben.
“Dole ne kuma ya tabbatar da kashi daya bisa uku na kuri’un da aka kada a kashi biyu bisa uku na dukkan jihohin tarayya da kuma babban birnin tarayya. Hakan ya zama wajibi.
