Connect with us

Labarai

Jam’iyyar APC Ta Dakatar Da Wani Shugaban Jam’iyyar A Jihar Zamfara

 

Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta dakatar da shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Bukkuyum a jihar, Shehu Buda-Nasarawa, bisa zargin cin zarafin jam’iyyar.

Shugabannin jam’iyyar a jihar sun kuma amince da nadin Tafa Nasarawa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na riko a karamar hukumar.

Jaridar DailyNigerian ta rawaito cewa Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ya fitar a Gusau ranar Asabar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Don sanar da jama’a an dakatar da shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Bukkuyum, Shehu-Buda Nasarawa.

“Kwamitin zartaswar jam’iyyar na jiha karkashin jagorancin Alhaji Tukur Danfulani ya amince da nadin Alhaji Tafa Nasarawa a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC na yankin.

“Nadin ya fara aiki nan take, kuma an umurci tsohon shugaban da ya mika duk kadarorin jam’iyyar a hannun shugaban riko har sai an kammala bincike a kansa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet