Wasanni
Jin rauni ya haramta wa Benzema shiga gasar kofin duniya
Rauni da ɗan wasan gaba na ƙasar Faransa kuma gwarzon ɗan ƙwallon duniya da ya lashe kyautar Ballon ta bana Karim Benzema, ya sake samu, ya janyo masa sanadiyyar rashin samun damar buga gasar Kofin Duniya da za a fara gudanarwa a ƙasar Qatar yau Lahadi.
A jiya Asabar ne Benzema mai shekara Talatin da huɗu a duniya ya sake samun rauni yayin da yake atisaye cikin tawagar Faransa.
BBC ta ruwaito cewa, hakan ne zuwa ne kwanaki kaɗan bayan murmurewar ɗan wasan daga raunin da ya samu a baya.
A ranar Talata mai zuwa ne ƙasar Faransa za ta fara buga wasa a gasar ta cin kofin Duniya inda za ta ɓarje gumi da ƙasar Australiya.
Sai dai yayin da Karim Benzema ke ke bayyana damuwa kan rashin samun damar shiga gasar, shi ma mai horas da tawagar ƙasar Faransa Didier Deschamps, shi ma ya nuna alhini game da rashin Benzema a gasar.
