Labarai
Miji Ya Kai Karar Matarsa Gaban Kotu Bisa Zargin Auren Wani Mutumin A Asirce
Wani dan kasuwa, Victor Ora, a ranar Litinin din nan ya maka matarsa, a gaban wata kotun gargajiya da ke Jikwoyi Abuja, bisa zarginta da auren wani mutumin a sirri.
Victor, wanda ya shigar da kara a cikin takardar sakinsa, ya ce: “matata ta yi ƙaura daga gidanmu ba tare da sanar da ni ba. Da na same ta sai ta furta cewa ta auri wani mutum.
“A kan haka ne nake neman raba auren da ke tsakaninmu,” in ji shi.
Ya shaida wa kotun cewa surukar sa tana hana shi zuwa ganin dansa.
“Na samu labarin cewa dana yana tare da surukata, sai na je don na gan shi amma surukata ta ki yarda na gan shi.
“Ta sha alwashin sai bayan mutuwarta zan gan shi. Ina rokon wannan kotu mai daraja da ta raba auren ta kuma ba ni rikon dana,” ya roki.
Jaridar DailyNigerian ta rawaito cewa Alkalin kotun, Mista Labaran Gusau, ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba.
