Connect with us

Labarai

Wata Babbar Kotu Ta Umarci Hukumar Zabe Da Ta Koma Yin Rijistar Katin Zabe

Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta gaggauta dawo da yin rijistar katin zabe (CVR) har zuwa kwanaki 90 kafin babban zaben shekarar 2023.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Ekwo ya kuma umurci INEC da ta tabbatar da cewa ba a hana ‘yan Najeriya da suka cancanta damar samun katin zabe a zabe mai zuwa ba.

Ya ci gaba da cewa hakki da tsarin mulki ya rataya a wuyan mahukanta zaben ne su samar da isasshen tanadi domin gudanar da zaben kamar yadda dokokin Najeriya suka tanada.

Wani Anajat Salmat da wasu mutane uku sun kai karar INEC gaban kotu inda suka ce hukumar zabe ba za ta iya dakatar da rajistar katin zabe ba sabanin yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Sun bukaci kotun da ta umarci hukumar zaben da su ci gaba da gudanar da atisayen kamar yadda dokar kasar ta tanada.

A watan Yuli ne hukumar INEC ta dakatar da yin rijistar katin CVR bayan tsawaita wa’adin wata daya biyo bayan korar da babbar kotun tarayya ta yi na yin watsi da karar da kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta shigar da ke neman tsawaita aikin har zuwa ranar 30 ga Yunin 2022.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet