Labarai
Buhari Zai Halarci Taron Kaddamar Da Wani Littafi Na AU A Jamhuriyar Nijar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis zai fara wata ziyarar aiki a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, kamar yadda mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya bayyana a wata sanarwa a ranar Larabar nan.
Shugaban zai halarci taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka kan bunkasa masana’antu da habaka tattalin arziki, da kuma wani zama na musamman kan ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka.
Buhari zai kuma halarci taron kaddamar da Littafin Faransanci mai suna ‘Muhammadu Buhari: Kalubalen Shugabanci a Najeriya’.
