Connect with us

Labarai

Gwamna Ganduje Ya Rattaba Hannu A Dokar Masu Bukata Ta Musamman

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya Sanya hannu Kan dokar masu bukata ta musamman.

Da yake Sanya hannu Kan dokar a yau Talata, yayin zaman majalisar Zartaswa na gwamnatin jihar Kano, Gwamna Ganduje Yace Sanya wa dokar hannu zai baiwa masu bukata ta musamman damar a dama dasu a kowanne fanni na rayuwa .

Ganduje Yace za’a zabo Wakilin da zai jagoranci sashin masu bukata ta musamman daga cikinsu, inda yayi Kira dasu yi rijistar sunayensu a kananan hukumomin su, domin gwamnati zata tantance wadanda za’a koyawa sanaoin dogaro dakai.

Jaridar KAKAKIHAUSA ta rawaito cewa Gwamnan ya Kuma ce gwamnati ta bada damar Samar da yanayi na musamman a makarantu da ma’aikatu domin dacewa da rayuwar ta masu bukata ta musamman.

Gwamnan ya Sanya hannun Kan dokokin Zirga-zirgar motoci da dokar da zata kula da kasuwar Abubakar Rimi da Singa da Galadima da Kuma dokar muhalli wadda zata hana bayan gari a bainar jama’a da dokar sauyawa jami’ar Wudil suna zuwa jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dan gote.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet