Labarai
IGP Ya Yi Alkawarin Samar Da Ofisoshin Yan Sanda Na Zamani A Duk Jihohin Kasar Nan
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Kasar nan, IGP Usman Alkali Baba, ya yi alkawalin cewa za a kina ofisoshin ‘yan sanda na zamani irin wanda ‘yan sandan ke ginawa a fadin kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Talata yayin da yake kaddamar da daya daga cikin sabbin gine-gine na zamani a Madi, karamar hukumar Ilorin ta yamma.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kaddamar da aikin, IGP ya ce ginin zai kara kusantar da aikin ‘yan sanda ga jama’a.
“’Yan sanda za su yi aiki a karkashin yanayi mai kyau ta fuskar muhallin ofishin, wurin zama mai kyau wanda hakan zai ba su damar samar da karin ayyuka.
“Za su kasance a nan dare da rana 24/7. Ofiahin yan kusa da jama’a wanda zai share musu hawaye. Muna tsammanin za a sami ƙarin sadaukarwa, ƙarfafawa da ingantaccen isar da ayyuaka.
Ya kara da cewa, “Za a yi irin wannan tsarin a jihohi da dama na tarayya saboda gwamnatin tarayya za ta so shi a dukkan sassan kasar nan.”
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, a wajen taron, ya ce za a kara ware wa dukkanin hukumomin tsaro kudade a kasafin kudin jihar na gaba.
