Labarai
Muslim Muslim: APC ba za ta ci Zaɓen baɗi ba- Babachir Lawan
Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya kuma jigo a jam’iyyar APC Mista Babachir Lawan ya ce, jam’iyyar ba za ta ci zaben shugaban ƙasa ba a Zaɓen baɗi sakamakon zaɓar mataimaki Musulmi da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Bola Tinubu ya yi.
Mista Babachir ya bayyana hakan ne a ganawarsa da BBC.
Haka kuma ya ce, sun yi iyaka bakin ƙoƙarinsu domin ganin Tinubu tunda shi Musulmi ne, ya samu takara, amma daga baya sai suka fahimci ya yi musu rufa-rufa game da abokin takara ko mataimakinsa, lamarin da ya sa suka juya masa baya.
Ya kuma ce, jam’iyyar APC ba za ta kai labari ba a zaben shugaban kasar, kuma zai iya faden jihohin da Bola Tinubu zai iya cin zabe da kuma wadanda ba zai ci ba.
Ya ce, ‘‘Ni dai kam ba na Bola Tinubu yanzu. Ni ba na Muslim-Muslim ticket.’’
‘’Shi Bolan ne bai zabe mu ba ya zabi inda yake so ya je, mun kuma gaya masa can daman ba za mu zabe shi ba in ya yi Muslim-Muslim ticket.’’ In ji shi.
Tsohon Sakataren gwamnatin tarayyar ya ƙara da cewa PDP sun zo sun tattauna da su, kuma sun yarda za su yi musu abin da suke soi dan suka hada kai saboda haka sun yarda za su yi musu.
