Connect with us

Labarai

2023: Buhari Zai Murƙushe Ƴan Ta’adda Kafin Ya Gama Mulki – Femi Adesina

 

Mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai a ranar Laraba Femi Adesina ya bayyana cewa shugaban nasa zai kawo karshen duk wani kalubale na rashin tsaro kafin mika mulki ga wanda zai gaje shi a shekarar 2023.

Adesina ya ce za a dakatar da sace-sacen mutane da ‘yan fashi da makami kafin zabe mai zuwa.

Ya yi magana ne a Abuja ranar Laraba a taron shekara-shekara kan tsaro da sadarwa.

Mai magana da yawun shugaban kasar wanda ya jagoranci taron ya bayyana cewa alkalumma a fadin kasar sun tabbatar da cewa sannu a hankali kasar na shawo kan kalubalen rashin tsaro da Buhari ya gada.

Adesina ya yi tsokaci kan wasu sassan kasar da ke fama da rikici inda ya kara da cewa lamarin ya lafa cikin ‘yan watannin da suka gabata.

“Ko da yake wasu, saboda dalilan da aka fi sani da su, ba za su yarda ba, amma gaskiya da gaskiya ita ce Najeriya na shawo kan kalubalen rashin tsaro.

“Al’amarin ya lafa, kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar kasar fiye da yadda ya gada.

“Tsaro na kara samun sauki kullum kuma shugaba Buhari zai yi nasara a yakin kafin ya mika mulki a shekara mai zuwa,” in ji shi

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet