Labarai
Gwamantin Tarayya Ta Tsawaita Ranar Dawowar Aikin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna
Gwamnatin tarayya ta sanar da tsawaita wa’adin dawowar aikin layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.
Ministan Sufuri Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna ranar Lahadin nan a wani rangadin da ya kai don duba shirye-shiryen dawowar layin dogon na Abuja zuwa Kaduna kafin ya fara aiki.
Sai dai bai bayar da takamaiman ranar da za a ci gaba da gudanar da aikin sufurin ba amma ya kara da cewa ba zai wuce mako guda ba.
A cewar ministan, gwamnatin tarayya ta bullo da wani sabon tsarin siyan tikitin, wanda a cewarsa shi ne mafarin daukar mataki kan matsalar tsaro wanda zai baiwa gwamnati damar tantance wadanda ke hawa jirgin a kowane lokaci.
Idan za a iya tunawa dai a makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna zai koma aiki a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2022.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa An dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna na wani dan lokaci watanni takwas da suka gabata, lokacin da ‘yan ta’adda suka tayar da bama-baman da suka toshe titin jirgin samfarin AK-9 a lokacin da yake kan hanyarsa daga Abuja zuwa Kaduna.
‘Yan ta’addan sun kashe mutane tare da yin garkuwa da fasinjoji sama da 60, wadanda daga bisani suka sake su.
