Labarai
Mai horas da ƴan wasa Herve Renard ya ƙaryata bai wa ƴan wasan Saudiyya motoci ƙirar Rolls Royce
Mai Horas da ƴan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Saudiyya Herve Renard, ya musanta rahotannin da ke cewa yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, zai bai wa ɗaukacin tawagarsa kyautar mota kirar Rolls Royce bisa nasarar da suka yi da Argentina babu ƙamshin gaskiya.
Awani rahoto da jaridar New York Post ta fitar, tace kocin ya ce babu kanshin gaskiya kan rahoton.
Renard ya ce, “Babu wani gaskiya game da wannan rahotannin, muna matakan tarayya da ma’aikatar wasanni kuma ba lokacin da za a samu wani abu bane yanzu.
Wasa ɗaya kawai muka buga, muna da wasanni biyu masu matukar muhimmanci [matakin rukuni] kuma muna fatan samun nasara a wasu.”
Abinda kawai ke da kyau a ƙarshen wannan rukunin shine mu zamo na 1 ko na 2. “, in ji Renard.
Shi ma Saleh al-Shehri wanda ke buga gaba a ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Saudiyya ya tabbatar da cewa rahoton karya ne, yana mai cewa, “Ba gaskiya ba ne, mun zo nan ne don hidimtawa kasarmu kuma mu yi iya kokarinmu.
Jaridar New York Post ta bada rahoton cewa, da’awar ta fito ne daga shafin Twitter na wani likitan haƙori ɗan ƙasar Pakistan wanda ba shi da masaniya.
