Connect with us

Labarai

INEC Ta Sha Alwashin Gudanar Da Zaben 2023 Duk Da Harin Da Ake Kaiwa Ofisoshinta

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta ce hare-haren da ake kaiwa ofisoshinta a baya-bayan nan ba zai hana ta gudanar da zaben 2023 ba.

Shugaban hukumar ta INEC na kasa Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar Tarayyar Afirka na musamman kafin zabe a karkashin jagorancin Phumzile Mlambo-Ngcuka a ranar Litinin din nan a Abuja.

Yakubu, wanda ya amince da cewa an yi asarar wasu kayayyakin zabe a hare-haren, ya ce INEC za ta maye gurbinsu gabanin lokacin zaben.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa An kai wa ofisoshin hukumar hari a jihohi uku – Ogun, Osun da kuma Ebonyi cikin makonni uku da suka gabata.

Mista Yakubu ya ce kaddamar da tsarin amfani da na’urar Bimodal Voter Accreditation System (BVAS) da kuma Results Viewing Portal (IReV) don tantance masu kada kuri’a da kuma loda sakamakon PU a kan lokaci ya zo karshe.

Yakubu ya ce babu gudu babu ja da baya kan tura wadannan fasahohin domin wata bukata ce ta doka ta tilasta wa INEC yin hakan.

Ya ce a tsakanin watan Agustan 2020 zuwa Yuli 2022, an yi amfani da fasahohin na kusan 105 a zabukan fitar da gwani da suka hada da zaben gwamnonin Anambra, Ekiti da Osun.

Shugaban na INEC ya ce kungiyar jam’iyyun siyasa, (IPAC) ta kuma tabbatar da ingancinsu wajen gudanar da zabe.

Yakubu ya ce duk da cewa INEC na iya samun ‘yar cikas nan da can amma za a cigaba da yin abun da ya kamata don gudanar da zaben 2023.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet