Labarai
Yakubu Ya Tabbatarwa ‘Yan Najeriya Cewa Hukumar INEC Za Ta Farfado
Gabanin babban zaben shekarar 2023, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za ta farfado daga hare-haren da aka kai kan cibiyoyinta.
Da yake jawabi a taron kaddamar da kwamishinonin zabe na yankuna da aka gudanar a Legas ranar Laraba, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, “hakkinmu shi ne gudanar da zabe. Ina so in tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za mu farfado daga wadannan hare-haren.
“Za a maye gurbin kayan da aka bata amma akwai iyaka ga ikonmu na ci gaba da maye gurbin abubuwan da suka bata ko suka lalace cikin kwanaki 86 kacal kafin babban zaben.”
A cikin makwanni uku an kai hare-hare guda biyu kan ofisoshin INEC a jihohin Ogun da Osun. Ko da yake INEC ta ce an kai wa ofishinta na Ebonyi hari a ranar Lahadi, amma ‘yan sanda sun ce gobara ce ta tashi a wurin.
Makwanni biyu da suka gabata, hukumar ta koka da yadda ake kai hare-hare a ofisoshinta, inda ta ce adadin ofisoshin INEC da wasu ‘yan daba suka kai wa hari sun kai 50. An samu rahotannin hare-haren a jihohi 21.
Domin dakile sake afkuwar wadannan hare-hare, Yakubu ya ce hukumar za ta yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa Shugaban na INEC ya yi kira da a kama masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu, “domin kada masu yin barna da kone-kone su ji cewa halayyar ta karbu a kasarmu”.
