Labarai
Gwamnoni Suna Satar Kudaden Kananan Hukumomi, Inji Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din nan ya nuna cewa gwamnoni suna satar kudaden kananan hukumomi.
Shugaban, wanda ya yi magana da kakkausar murya bayan ya gabatar da jawabinsa a zauren taron shugaban kasa ga mambobin Senior Executive Course 44 (2022) na National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS) a gidan gwamnati, ya jaddada cewa mutuncin mutum yana da tushe a cikin ayyukan gwamnati.
Ya tuna da wani misali na yadda gwamnan jiha zai karbi kaso a madadin kananan hukumomin jihar sa sai ya mika rabin wannan kason ga shugabannin majalisar kansuloli.
Wadannan ayyuka, in ji shi, sun nuna irin ayyukan cin hanci da rashawa da a yanzu ke zama alamr Najeriya wajen raba albarkatun da ake baiwa kananan hukumomi, wanda hakan ke kawo cikas ga ci gaba.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa Buhari a jawabinsa ya taya mambobin babbar darasin 44 murnar kammala kwas din da suka yi. Ya kalubalance su da su farfado da karfafa jagoranci a matakai daban-daban na ci gaba.
