Connect with us

Labarai

Jihar Bauchi Ta Sami Masu Cutar HIV Sama Da 2,000 A Shekarar 2022

 

Ma’aikatar lafiya ta jihar Bauchi ta bayyana cewa jihar ta samu sabbin mutane sama da 2,000 da suka kamu da cutar kanjamau a shekarar 2022 a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Sabiu Abdu Gwalabe, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis din nan yayin wani taron manema labarai na bikin ranar yaki da cutar kanjamau HiV ta duniya a jihar.

Ya bayyana cewa kashi 98 cikin 100 na sabbin masu kamuwa da cutar sama da 2,000 na da nasaba da jiyya a cikin wannan shekarar kadai.

Ya kara da cewa, “Wannan shi ne adadi mafi yawa na sabbin masu kamuwa da cutar a kowace shekara a jihar, wanda ya faru ne saboda kwazo da sabbin hanyoyin da ma’aikatanmu da abokan huldar mu suka dauka.

“A halin yanzu jihar tana da kimanin mutane kusan 30,000 da ke dauke da cutar kanjamau.

“A cikin 30,000, an riga an gano 29,160 daga cikinsu wanda ke wakiltar kashi 97 cikin 100. Hakazalika, 27,639 na wadanda suka san matsayinsu na dauke da cutar kanjamau a halin yanzu suna kan magani wanda ke wakiltar kashi 95 cikin dari.”

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Sai dai ya bayyana cewa a hankali an samu raguwar yaduwar cutar kanjamau a jihar zuwa kashi 0.4 kacal a shekarar 2019 wanda ya yi kasa da yawan al’ummar kasar da ya kai kashi 1.5 cikin dari kusan mutane miliyan 3 da ke dauke da cutar kanjamau a kasar nan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet