Labarai
Zaben Yara: Za Mu Ci Gaba Da Tsaftace Rijistar Zabe — Shugaban INEC
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ya ce hukumar za ta ci gaba da tsaftace rajistar masu kada kuri’a domin dakile zaben wadanda ba su kai shekarar ba.
Yakubu ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da ‘yan jarida a Legas ranar Juma’ar nan.
“Muna kokarin ganin mun kawar da zaben kananan yara da kuma kada kuri’ar da ba ta dace ba.
“Don haka ne muka shirya rajistar ga duk ‘yan Najeriya da suka mallake ta. An lika rajistar ne a dukkan rumfunan zabe da mazabun da ke kananan hukumomi 774 na Najeriya domin bayyanawa ‘yan Najeriya karin haske da rashin amincewarsu.
“Yanzu muna tattara ikirari da rashin amincewa da ’yan Najeriya don yin aiki a kansu da kuma tabbatar da cewa muna ci gaba da tsaftace rajistar.
“Ina tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da wannan aikin domin rajistar INEC wani abu ne na kasa da ya kamata ‘yan Najeriya su yi alfahari da su,” inji shi.
Dangane da yiwuwar gudanar da zabe a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula, Yakubu ya ce INEC na aiki da hukumomin tsaro a kan hakan.
“A fili yake alhakin da ya rataya a wuyanmu, wato gudanar da zabe mai zuwa a dukkan sassan kasar nan. Hukumomin tsaro sun samar da tsaro.
