Connect with us

Labarai

Hukumar INEC Ta Tabbatar Da Sake Kaiwa Ofisoshinta Hari Sau Biyu Cikin Kwana Uku

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) a ranar Lahafin nan an sake kai wani harin a ofisoshinta da ke jihar Imo.

Yayin da harin farko ya faru a ranar Alhamis, na biyun ya zo ne bayan sa’o’i 72.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

Ya ce an kai harin na baya-bayan nan a ofishinta da ke karamar hukumar Oru ta Yamma a jihar Imo da misalin karfe 4:00 na daren ranar Lahadi.

Harin na baya-bayan nan, in ji shi, ya zo ne kwanaki uku bayan da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai farmaki ofishin hukumar a karamar hukumar Orlu.

“Kwamishiniyar zabe (REC) reshen jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu, ta ruwaito cewa an kai wa ofishinmu da ke karamar hukumar Oru West hari da misalin karfe 4.00 na dare yau Lahadi 4 ga watan Disambar, 2022,” inji shi.

“Harin ya shafi dakin taro ne inda aka lalata kayayyakin ofis da kayan aiki. Duk da haka, sauran wurare masu mahimmanci ba ta shafi su ba.

“Za a iya tunawa cewa a ranar Alhamis 1 ga watan Disambar 2022, an kai hari ofishinmu da ke karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.”

A cewar Okoye, harin na ranar Lahadi shi ne irinsa na bakwai da ake kai wa cibiyoyin alkalan zabe a jihohi biyar na tarayya cikin watanni hudu da suka gabata.

Ya kara da cewa hukumar ta damu matuka game da “sakamakon abin da ake ganin tamkar wani shiri ne na kai hari kan cibiyoyinta a fadin kasar nan kan gudanar da zabe musamman da kuma ayyukan zabe baki daya.”

Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa Kwamishinan na INEC na kasa ya bayyana cewa an ja hankalin hukumomin tsaro kan wannan sabon lamari domin bincike da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet