Uncategorized
Neymar zai fafata a wasan Brazil da Korea ta Kudu
Kocin tawagar kwallon kafar brazil, Tite ya tabatar da cewa Neymar zai samu fafatawa a wasansu da Korea ta Kudu a zagaye na biyu na gasar kofin duniya.
Dan wasan gaban mai shekaru 30 bai samu fafatawa a wasanni biyu na matakin rukuni ba sakamkon rauni da ya samu a idon sawunsa na dama a wasansu na farko da suka gwabza da Serbia.
Brazil, tawagar da tun kafin gasar ake kallo a matsayin daya daga cikin wadanda za su iya lashe gasar ta samu hayewa zagaye na gaba daga matakin rukuni da saura wasa daya, kuma ta jagoranci rukunin G duk da doke ta da Kamaru ta yi.
Kocin Brazil, wanda ya tabbatar da kasancewar Neymar a cikin wadanda za su yi wasan yau ya ce ko a ranar Lahadi sai da dan wasan ya yi atisaye, kuma ya yi shi da kyau.
A cikin minti na 80 ne aka sauya dan wasan gaban na Paris St Germain a wasan da Brazil ta doke Serbbia da ci 2 da nema, bayan wani duka da Nikola Milenkovic ya mai a kafarsa ta dama.
