Uncategorized
Kocin Faransa ya haramta ‘yan wasan tawagar kasar sanya sarkar wuya
Didier Deschamps zai haramta sanya Sarkar wuya ga ‘yan wasan tawagar Faransa a wasan su na kusa dana karshe da za su buga a ranar Asabar da Ingila, inda ya ce Jules Kounde ya yi sa’a na rashin gamuwa da fushinsa bayan da alkalin wasa ya umurce shi ya cire Sarkar wuya ta zinare da ya saka a yayin wasan da suka lallasa Poland 3-1.
Alkalin wasa Jesus Valenzuela ya tilasta wa dan wasan bayan na Barcelona cire sarakar wuya da yake sanye da ita a wasan zageye na biyu a filin wasa na Al Thumama bayan da ya hango ta.
Daya daga cikin mataimakan Deschamps ne ma ya taimaka wa dan wsan wajen cire sarakar, sakamakon yadda ya gaza cirewa da kansa.
Ko da yake lamarin bai yi tasiri a kan wasan na Faransa ba, Deschamps ya ce hakan ba zai sake faruwa ba, saboda daga yanzu babu dan wasan da zai sanya Sarkar wuya a cikin fili.
