Connect with us

Labarai

Ban san adadin dukiyar da na tara ba, amma dai na samu kuɗi ne ta hannayen jari- Tinubu

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, bai san adadin dukiyar da ya tara ba.

Tinubu, ya bayyana hakan ne ranar Talata a ganawarsa da gidan rediyon BBC.

Haka kuma ya bayyana cewa ya samu kuɗaɗensa ne ta hannayen jari.

Tinubu wanda ya yi magana a kan batutuwa da dama, ya yi jawabi kan matsalar tsaro, ya kuma bayyana cewa har yanzu kasashen Yamma ba su ji dadin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba, dalilin kenan da ya sa suke kin sayar wa da gwamnatinsa makamai.

Sai dai ya ce ya yi imanin Buhari ya yi iya bakin kokarinsa a matsayinsa na shugaban kasa, don haka yayi iya kokarin sa wajan saisaita al’amuran kasar.

Tinubu, wanda ya ce yana da kwarin guiwa wajen kare irin nasarorin da Buhari ya samu a fannin tsaro, ya yi ikirarin cewa gwamnati mai ci, ta kawar da tashe-tashen hankula a kasar nan daga bala’in da suke fuskanta a baya.

Yayin da yake amsa tambaya kan yadda ‘yan Najeriya ke shan wahala a karkashin gwamnati mai ci, ya ce shi Bola Tinubu ne ba Buhari ba, don haka idan yayi nasara lamarin zai sha bamban.

Dan takarar na jam’iyyar APC ya bayyana akasarin wadanda ke tambayar tushen arzikinsa ko kuma yi masa tambayoyi a matsayin masu hassada.

“Na gaji dukiya mai tarin yawa kuma Ina jujjuyata ta hanyar kasuwanci iri daban daban,” in ji shi.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana cewa abin da zai sa a gaba shi ne tsaro da sake farfado da tattalin arzikin kasar tare da mai da hankali kan samar da ayyukan yi idan aka zabe shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet