Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudurinta Na Magance Sauyin Yanayi Da Ambaliyar Ruwa

 

Gwamnatin jihar Kano jaddada kokarin ta na magance matsalar sauyin yanayi, inda ta ce tayi kokarin sanya ayyuka cikin kasafin kudin badi da zasu dakile matsalar a jihar.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso, ne ya bayyana haka yayin da yake kare kasafin kudin ma’aikatarsa a gaban kwamitin majalisar dokokin jihar.

Ya ce rahoton kwamitin da suka kafa ya bayyana cewa duk da cewa gine ginen da a keyi akan magudanan ruwa da zubar da shara na daga cikin musabbabin samun ambaliyar ruwa, amma babban dalilin shine sauyin yanayi da aka samu a fadin duniya.

Da yake jawabi shugaban kwamitin muhalli na majalisar kuma dan majalisa Mai wakiltar Takai, Musa Ali Kachako, ya ce an warewa ma’aikatar kudi Naira Biliyan uku da miliyan dari takwas da tamanin da shida don gudanar da ayyukan ci gaban al’umma.

Ya kuma bayyana irin sauye sauyen da suka yiwa kasafin kudin ma’aikatar muhallin na shekara mai zuwa.

A nasa jawabin Shugaban kwamitin muhallin Musa Ali Kachako ya ce an sanya batun gina bandakuna a cikin kasafin kudin na badi domin amfani al’umm.

KAKAKIHAUSA ta rawaito cewa an sami ambaliyar ruwa a jihar Kano da ma fadin kasar nan har da duniya baki daya irin wanda ba a taba gani ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet