Uncategorized
Qatar 2022: Ajiye Ronaldo a benci ya haifar wa Portugal da mai ido
Kocin Portugal Fernando Santos ya ajiye Ronaldo a benci a wasan zagayen ‘yan 16 da suka fafata da Swizerland, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, tun da wanda ya maye gurbinsa, Goncalo Ramos ya taka rawar gani, inda ya ci kwallaye 3 rigis a wasan.
Tun da farko Santos ya bayyana rashin jin dadinsa a kan irin yadda Ronaldo ya nuna ya fusata sakamakon sauya shi da aka yi a wasansu da Korea ta Kudu, kuma wannan ne karo na farko a cikin wasanni 31 tun da shekarar 2008 da ba a fara wasa da Ronaldo a wata babbar gasa ba.
Portugal sun buga wasan ba tare da suna jin kewar dan wasan mai shekaru 37 ba, a yayin da matashin dan wasan mai shekaru 21, wanda ke wasa a Benfica, Goncalo Ramos ya ci kwallaye 3 rigis a karon farko a babbar gasa.
Wannan nasarar da Portugal ta samu ya sa ta tsallaka zuwa matakin wasan daf da kusa da na karshe, kuma za ta hadu ne da Morocco, wadda ta doke Spain a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Ronaldo, wanda ya shigo daga baya, ya saka kwallo a raga, amma alkalin wasa ya ce ba ta ciwu ba, saboda ya yi satar fage.
