Connect with us

Kasuwanci

Wata Gobara Ta Kone Tankoki Biyar Dauke Da Lita 20,400 Na Man Dizal

Wata gobara ta kone wani gini da ba a kammala ba da akw amfani da shi wurin ajiyar man dizal, inda ta kone tankokin guda biyar dauke da lita 20,400 na dizal a unguwar Farawa Kwanar Yashi da ke cikin birnin Kano a ranar Talata.

Lamarin dai a cewar hukumar kashe gobara ta jihar, ya faru ne sakamakon wani tartsatsin wuta daga injim janareta mai dauke da man dizal da ake amfani da ita wajen loda man dizal daga tankokin dizal zuwa wasu tankunan.

Kakakin hukumar a jihar, SFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce mutane uku ne suka makale a cikin mummunan lamarin amma duk an ceto su da ransu kuma an garzaya da su asibiti domin yi musu magani.

Ya ce hukumar su ya samu kiran gaggawa daga ma’aikatan da suka kai rahoton bullar gobarar a Kangon Saminu Farawa da ke hanyar Kwanar Yashi Maiduguri da misalin karfe 00:29 na dare.

“Da isar su, sun gano cewa wani gini da ba a kammala ba na kimanin 200 x 200 da aka yi amfani da shi a matsayin wurin ajiyar man dizel, kimanin tankokin dizal guda biyar dauke da kusan lita 20,400 na dizal, injin Lifan guda daya da janareta masu aiki guda uku.

“Da kyakkyawan namijin kokarin da mutanen mu suka yi, mun samu nasarar shawo kan lamarin tare da ceto tankunan man diesel guda uku, tankokin guda 9 tare da hana wutar bazuwa zuwa wasu wuraren.

Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Ya kara da cewa, “Yayin da mutum uku da suka makale, wato Mai Daura Sadi mai shekaru 24, Hassan Sadi da Iliyasu Sadi maj kimanin shekara 25 duk an ceto su da ransu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet