Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne, sun sace iyalan wani ɗan majalisar dokokin Jihar Zamfara a garin Jangebe da ke jihar.
BBC ta ruwaito cewa, ƴan bindgar da kuma ake ƙarfafa zaton masu garkuwa da mutane ne, sun yi dirar mikiya ne a gidan ɗan majalisar Aminu Yusuf Ardo ne a daren jiya Alhamis, inda suka sace matarsa da dukkan ƴaƴansu guda hudu waɗanda ƙanana ne.
Haka kuma ta ruwaito cewa, ɓata garin sun kuma sace wasu maƙwabtan ɗan ɗan majalisar kamar yadda wani mazaunin unguwar ya bayyana.
