Labarai
Cutar Maleria ta hallaka fiye da ƴan Najeriya 600,000- WHO
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana cewa kaso talatin da daya cikin dari na mutanen da zazzabin cizon sauro watau maleriya ya hallaka a duniya bara ƴan Najeriya ne.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin rahoton cutar wanda ta fitar ranar Alhamis ɗin makonnan.
Rahoton ya ce, duk da tasirin cutar Covid-19 da ake ci gaba da gani a halin yanzu, zazzabin cizon sauron na ci gaba da hallaka mutane a duniya.
WHO ɗin ta kuma ce cutar, ta hallaka mutane dubu dari shida da goma sha tara a bara, bayan da ta kama mutane miliyan dari biyu da arba’in da bakwai, adadin da ya zarce na shekarar 2019.
Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanon Ghebreyesus, ya bukaci kasashen duniya da su tashi tsaye tare da kara kaimi wajen yakar cutar zazzabin cizon sauron, don kare rayukan al’ummarsu.
