Connect with us

Labarai

Jami’ar Bayero ta samu ƙarin sabbin farfesoshi 34

Jami’ar Bayero ta Kano, ta amince da yin ƙarin girma ga manyan malaman ta su Talatin da huɗu i zuwa matakin Farfesoshi da kuma maƙaddasan farfesoshi su Hamsin da shida.

Jami’ar ta amince da su ɗin ne a taron majalisar gudanarwar ta karo na shekarar 2020 zuwa 2021.

A wata sanarwa da muƙaddashin darakta gudanarwa ta jami’ar Binta Yahaya Kofar Na’isa ta fitar a juma’ar nan, ta ce an amince da ɗaga likkafar ne bayan amincewar zaman majalisar da aka gudanar ranar Alhamis.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa waɗanda aka ɗaga likkafar ta su zuwa mukamin Farfesa sun hada da tsohon shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i, Dakta Nasir Isa Fagge a matsayin Farfesa a fannin kimiyyar nukiliya da Dakta Usman Ibrahim Abubakar, Farfesa a fannin yaɗa labarai da kuma Dokta Salihu Lawal, shugaban sashen ci-gaba da Ilimi a matsayin Farfesan Nazarin Addinin Musulunci.

Sanarwar ta ce, sauran wadanda aka gabatar a zaman sun hada da Dokta Sani Malami Farfesa a fannin harhada magunguna; Dr Musa Njidda Farfesan Kula da harkokin Wasanni; Dokta Bello Ibrahim Farfesa na Nazarin Laifuka da Tsaro; Dr Kabir Bello Farfesa a fannin ilimin zamantakewa Dr Ya’u Musa Dantata Farfesa na Ilimin Bukatu na Musamman da Dr. Aliyu Salisu Barau Farfesa na Ci gaban Birane da Gudanarwa da Dr Ibrahim Tajo Siraj Farfesa na ilimin sinadaran Inorganic Chemistry.

A cewar sanarwar, wadanda aka daga likafar su zuwa matsayin Mataimakin Farfesa sun hada da Dr Bashir Aliyu Umar Nazarin Musulunci; Dr Hafsat Umar Abdullahi Ilimi; Nura Ibrahim Bayanai da Nazarin Sadarwa; Hadiza Jummai Ibrahim Aikin jarida; Maryam Umar Moukhtar Aikin Jarida; Bala Boyi Bukata Bangaren lnjiniyancin jone jonen lantarki; Mohammed Mamodu Maina Noma da harkokin muhalli da Abdullahi Yahuza Zainawa Kimiyyar Siyasa.

Sanarwar ta ce, ”Dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki daga ranar 1 ga Oktoba, 2021.

Ya ce sauran malaman jami’o’in da suka samu karin girman zuwa matsayin Farfesa, Dokta Suwaiba Sa’id Ahmad, Darakta, Cibiyar Nazarin Jinsi; Dr. Kabir Bello Dungurawa, Shugaban Kano Polytechnic da Dr. Aliyu Dahiru Mohammed Na bangaren tattaki da sauransu.

Cikin waɗannan karawa girma zuwa matsayin Mataimakin Farfesa wanda zai fara aiki daga Oktoba 2020 kuma sune; Dr Ali Abdullahi Noma; Dr Auwal Sani Salihu Likitan tabin hankali; Dr Zaharaddeen Garba Habib Likitan kulada masu tabin hankali da Dr Musa Usman Umar Likitan kulada masu tabin hankali.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet