Uncategorized
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai je Qatar a ranar Laraba domin halartar wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya Faransa za ta buga da Morocco.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai je Qatar a ranar Laraba domin halartar wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya Faransa za ta buga da Morocco.
Kungiyar kwallon kafar Faransa za ta fafata da kungiyar kwallon kafar Morocco ranar Laraba a wasan daf da na karshe a gasar cin kofin Duniya da ke gudana a Qatar bayan nasarori da kungiyoyin suka samu.
Faransa ta lallasa Ingila da ci 2 da 1, yayinda Morocco dake wakiltar nahiyar Afrika, wanda shine karo na farko da Afirka ta kai wannan mataki ta doke Portugal da ci 1 mai ban haushi duk da kasancewar tauraron kasar Christiano Ronaldo cikin tawagar da suka fafata.
A birnin Paris na kasar Faransa zuwa wasu manyan birane na nahiyar Afrika da suka hada da Alkha’ira, Rabat ;Doha dubban magoya bayan Faransa da Morocco sun sun gudanar da bukukuwan murna.
Ministan wasanni Amélie Oudéa-Castera ta tabbatar da cewa, shugaba Macron zai isa Qatar ranar Laraba.
Faransa ta rugumi yan kasar Morocco da dama inda wasu ke kallon wannan wasa tsakanin Faransa da Morocco tamkar wasa tsakanin mahaifi da mahaifiya ne
