Labarai
IGP Ya Zargi ‘Yan Siyasa Da Wasu Mutane Da Hannu A Kai Hari Ofisoshin INEC
Babban sufeton yan sandan Kasar nan Usman Baba ya zargi ‘yan siyasa da wasu manyan mutane da hannu a hare-haren da ake kaiwa jami’an hukumar zabe mai zaman kanta a sassan kasar nan.
IG, wanda ya samu wakilcin mataimakin sufeto Janar na sashen ayyuka, Dandaura Mustapha, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai da ke binciken hare-haren da aka kai kan kadarorin INEC a fadin kasar nan.
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare kan kadarorin hukumar zabe na iya kawo cikas ga babban zaben 2023.
Baba ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya, kasancewar ita ce ke jagorantar harkokin tsaro a cikin gida da kuma zabe gaba daya, a kodayaushe tana kan karagar mulki, inda ya ce, “Duk abin da ya faru, hakkin ‘yan sanda ne su kare nan da can.
“An fara yakin neman zaben kuma abin da muka gane da farko shi ne rikicin tsakanin jam’iyya da jam’iyya. Mun fahimci cewa ’yan jam’iyyun siyasa na lalata allunan talla, fosta da ofisoshin yakin neman zabe a wasu sassan jihohin.
“Nan take muka sanar da kwamishinonin ‘yan sanda masu kula da oda, sannan muka ba su umarni karara cewa hakkin kowace jam’iyya ce ta shiga duk wani lungu da sako na al’umma da yakin neman zabe. Hakki ne da kundin tsarin mulki ya ba su, don haka ko kadan gwamnan jiha ko wani dan jiha bai kamata ya hana jam’iyyun siyasa yin kamfen dinsu ba.
“Yanzu mun zo kan hare-haren da aka kai a kan cibiyoyin INEC. A kwanakin baya, wadanda suka faru a Osun da Ogun, sai kuma a makon jiya a Ebonyi, Imo da Enugu; Sanin kowa ne cewa a shiyyar Kudu-maso-Gabas geopolitical zone, muna da batutuwan masu son ballewa ta IPOB da ESN.
“Wadannan kungiyoyi sun dukufa wajen ganin an hana zabe a yankin Kudu maso Gabas. Suna kai hari ga jami’an mu; sun kasance suna kwato makamai daga hannun jami’an tsaro, ba ‘yan sanda kadai ba har ma da sojoji da sauran kungiyoyin sa kai da ke wurin. Sun yi ta yin hakan, musamman a yanzu da aka dage takunkumin da aka sanya wa yakin neman zabe.
“Zaben na gabatowa cikin sauri kuma suna matsa lamba don ganin ba a gudanar da zabe a shiyyar Kudu maso Gabas ba.
