Labarai
Hukumar Zabe Ba Ta Da Wani Dalilin Da Zai Hana Ta Gudanar Da Zaben 2023 – Buhari
Shugaba Buhari ya ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ba ta da wani dalilin da zai hana ta gudanar da sahihin zabe a 2023 domin ya amince da duk abin da hukumar zaben ta bukata.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wani zama na tattaunawa mai taken, “Tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya,” wanda cibiyar nazarin zaman lafiya ta kasar Amurka USIP, da cibiyar International Republican Institute, da National Endowment for Democracy, suka shirya.
Ya kara da cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a shirye take ta gudanar da zaben 2023.
“INEC a shirye take domin na tabbatar an ba su duk kayayyakin da suka nema saboda bana son wani uzuri da gwamnati ta hana su kudaden.
“Tun daga shekarar 2015, gudanar da zabukan mu na ci gaba da inganta a kullum.”
“Daga babban zabukan shekarar 2019, zabukan fitar da gwani da aka gudanar a jihohin Edo da Ekiti da Anambra da Osun an gudanar da su cikin ingantattun yanayi wanda ya gamsar da ‘yan takara da masu kada kuri’a.
“Wannan shine abin da muke fata a 2023. Ta hanyar ayyukan sa ido na kasa da kasa, za a iya inganta amincin zabuka don tabbatar da yarda da sakamakon ga ‘yan takara da jam’iyyun siyasa.” “In ji shi.
