Connect with us

Uncategorized

Mbappe ya kafa tarihin jefa kwallaye mafi yawa a gasarcin kofin duniya

Dan wasan gaba na kasar Faransa Kylian Mbappe ya kafa wani sabon tarihi na jefa kwallaye 3 a wasan karshe na cin kofin duniya, abinda ya kai yawan kwallayen da ya jefa a gasar da aka kammala a Qatar zuwa 8.

A karawar da Faransa tayi da Argentina, Mbappe ya jefa kwallayensa guda 3 a mintina 80 da 81 da kuma 118 a wasan suka tashi 3-3, kafin ya kuma jefa kwallo guda a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Abokin hamayyarsa Lionel Messi ya jefa kwallaye guda 2 ne a karawar, wadanda ya jefa a mintina 23 da 108, abinda ya kawo adadin kwallayensa a gasar zuwa 7, kafin shima ya jefa guda a bugun daga kai sai mai tsaron gidan bayan sun tashi wasan 3-3.

Kwallayen da Mbappe ya jefa su suka taimakawa Faransa kai wasan zuwa bugun daga kai sai mai tsaron gida, a wasan da kasar Argentina sau biyu tana kama sahun gaba.

Wadannan kwallayen da Mbappe ya jefa sun sanya shi cikin jerin manyan ‘yan wasan duniya da suka jefa kwallaye a gasar cin kofin duniya irin su Vava a shekarar 1958 da 1962 da Pele a shekarar 1958 da 1970, sai Paul Breitner a shekarar 1974 da 1982 sannan Zinedine Zidane a shekarar 1998 da 2006.

A shekaru 23 Mbappe ya jefa kwallaye 15 a gasar cin kofin duniya a wasanni 17 da ya buga, wadanda suka zarce na zaratán ‘yan wasan Faransa irinsu Thierry Henry mai kwallaye 6 da Zinedine Zidane mai 5.

Ya zuwa yanzu ‘dan wasan Jamus Miroslav Klose ke rike da tarihin jefa kwallayen da suka fi yawa wadanda suka kai 16 a gasa 4 da ya halarta.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet