Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Koka Da Yadda Likitoci Suke Guduwa Kasar Waje
Mr Ekumankama Nkama ya koka da yadda ake fama da karancin likitoci, ma’aikatan jinya da sauran kwararrun likitoci a asibitocin gwamnati a dukkan matakai na kananan hukumomi, jiha da tarayya a Najeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude rukunin gadaje na kulawa da jinya, da sashin kula da yara, a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas a karshen mako.
Nkama ya ce LUTH da sauran manyan cibiyoyin kiwon lafiya na fuskantar karancin kwararrun likitocin, wanda hakan ya yi tasiri wajen haifar da damuwa a tsakanin yan kasa.
Ministan Wanda ya samu wakilcin daraktan shirin yaki da cutar daji na ma’aikatar, Dokta David Atuwo, ya ce, “Wannan matsala na yin illa ga ayyuka a asibitocinmu, har ta kai ga an rufe wasu sassan saboda rashin ma’aikatan da za su iya kula da su.”
Nkama ya kara da cewa ma’aikatar lafiya ta tarayya tare da wasu jami’an gwamnati da suka hada da ofishin shugaban ma’aikatan tarayya na aiki tukuru don ganin an maye gurbin ma’aikatan da suka fice cikin gaggawa ba tare da wata matsala ba.
Ministan ya ci gaba da cewa kaddamar da ayyuka guda uku ya nuna kwazon hukumar gudanarwa, da ma’aikatan LUTH a tsawon shekaru da kuma samun nasarar da ake samu a yanzu.
Ya bayyana ayyukan a matsayin shaida kuma abin alfahari, musamman ga babban Daraktan lafiya mai barin gado.
