Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranar Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun Litinin 26, Talata 27 ga watan Disamba, 2022 a matsayin rana hutun kirsimeti da ranukun raba kyaututtuka.

Kazalika ta ayyana Litinin 2 ga watan Janairu, 2023 a matsayin ranar hutun bukukuwan sabuwar shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dr Shuaib M.L. Belgore, babban sakataren ma’aikatar, a ranar Alhamis.

A lokacin da yake taya kiristoci da daukacin ‘yan Najeriya mazauna gida da na kasashen waje murnar bukukuwan Kirsimeti dana sabuwar shekara ta bana, Aregbesola ya gargade su da su yi koyi da Yesu Kiristi a cikin ayyuka da kuma bin koyarwarsa, musamman a kan bangaskiya, bege da kauna.

“Dole ne mu sanya rayuwar Yesu Kiristi cikin ayyukansa da koyarwarsa akan tawali’u, hidima, tausayi, haƙuri, salama da adalci, wanda haihuwarsa ke nuna. Wannan ita ce hanya mafi kyau don nuna Kristi da kuma bikin haihuwarsa,” in ji shi.

Ministan wanda ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro abubuwa ne guda biyu masu muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki da wadata, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin bukukuwan da suka dace wajen yin addu’o’in kawo karshen duk wata matsala ta rashin tsaro a kasar.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su tabbatar da zaben 2023 cikin nasara ta hanyar kada kuri’a cikin lumana tare da kaucewa duk wani abu da zai iya lalata aikin ta kowace hanya.

Aregbesola ya bayar da tabbacin cewa gwamnati ta samar da ingantattun matakai na tsaron rayuka da dukiyoyi, ya kara da cewa FG na fatan ‘yan Najeriya za su goyi bayan kokarin hukumomin tsaro ta hanyar samar da bayanai masu amfani da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.

Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu lura da harkokin tsaro, inda ya bukaci su kai rahoton duk wani mutum ko wani abu da suke da alaka da shi ga jami’an tsaro mafi kusa da kuma ta hanyar N-Alert na manhajar wayoyin Android da IOS.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. User Login

    08/06/2023 at 3:12 am

    The point of view of your article has taught me a lot, and I already know how to improve the paper on gate.oi, thank you. https://www.gate.io/fr/signup/XwNAU

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet