Connect with us

Labarai

Bukola Sarki Ya Yi Barazanar Maka Gwamna AbdulRazaq A Gaban Kotu

 

Dr Abubakar Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya yi barazanar daukar matakin kotu kan gwamna Abdulrahaman Abdurazaq na jihar Kwara.

Bukola Yayi wannan barazanar ne bisa zarginsa da yin sama da fadi da kudaden UBEC a lokacin da yake gwamnan jihar.

Gwamnan jihar Kwara, ya bayyana ikirarin da Gwamna Abdulrahaman Abdulrazaq ya yi na cewa ya wawure kudin asusun bai daya na ilimi, sannan kuma ya yi amfani da matsayinsa na shugaban majalisar dattawa wajen hana hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC binciken lamarin yana mai bayyana batun da cewa shifcin gizo ne kawai.

Bukola ya bukaci Gwamnan ya gaggauta janye wannan kalami na sa, cikin gaggawa ko kuwa ya dauki matakin shari’a.

Saraki a wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in yada labaran sa kan al’amuran cikin gida, Abdulganiyu Abdulqadir, ya yi barazanar cewa gwamnan yana da kwanaki bakwai kacal ya janye maganar ko kuma su hadu a kotu domin ya tabbatar da ikirarin nasa na karya.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin yakin neman zaben dan takarar sanatan APC na jihar Kwara ta tsakiya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet