Labarai
Gwamnatin Kogi Ta Bada Hutun Ma’aikata A Ranar Da Buhari Zai Ziyarci Jihar
Gwamnatin jihar Kogi ta ayyana ranar Alhamis 29 ga watan Disamba, 2022 a matsayin ranar hutu domin jihar za ta karbi bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wannan rana domin kaddamar da ayyukan da gwamna Yahaya Bello ya yi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kingsley Fanwo, ya raba wa manema labarai a Lokoja ranar Lahadi.
Gwamnatin jihar ta bukaci al’ummar jihar Kogi da su fito gaba daya domin tarbar shugaban kasar da kuma nuna karimcin da suka shahara wajen yin sa a jihar.
Kazalika, gwamnatin jihar ta bukaci dukkanin kungiyoyin kwadago da hukumomin tsaro da su tabbatar da cikakken bin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na tafiya jihar cikin lumana.
“Shugaban kasa kuma kwamandan rundunar sojojin Najeriya, mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, zai ziyarci jihar Kogi a ranar 29 ga watan Disamba, 2022 domin kaddamar da wasu ayyuka na gado a fadin jihar.
“Saboda haka da kuma tabbatar da shugaban kasa, gwamnatin jihar Kogi karkashin jagorancin Yahaya Bello na fatan sanar da ranar Alhamis 29 ga watan Disamba, 2022 a matsayin ranar hutu,” in ji sanarwar.
