Labarai
Magoya Bayan Jam’iyyar PDP Da NNPP Sun Sauya Sheka Zuwa APC A Zamfara
Jam’iyyar APC reshen Zamfara ta karbi wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da na sabuwar jam’iyyar NNPP da suka sauya sheka a jihar.
A ranar Litinin din nan ne tsohon Gwamna kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Abdul’aziz Yari ya tarbe su.
Mai magana da yawun Yari Dahiru Mafara ne ya bayyana sunayen mutanen a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Mutanen su ne Ibrahim Shinkafi, dan takarar Sanata na NNPP a Majalisar Dattawan Zamfara ta Arewa; Dan takarar majalisar wakilai, Shinkafi da Zurmi, Suleiman Garba.
Ma’ajin Jihar, Suleiman Galadi; Su ma shugabannin NNPP na kananan hukumomin Kaura-Namoda da Zurmi sun sauya sheka.
Sauran sun hada da Coordinator na wata gidauniyar yakin neman zaben gwamna a jam’iyyar PDP, Aminu Kanoma, da kuma Sakatare kuma Ma’aji, Aminu Saminu da Hajiya Umulkhairi Aminu.
Yari ya samu wakilcin shugaban kwamitin tuntuba da wayar da kan jama’a na majalisar Musa Zubairu.
Taron wanda ya gudana a Talatan Mafara ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na Zamfara, Tukur Danfulani da sauran sarakuna.
