Connect with us

Labarai

‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wani Mutum A Kotu Bisa Laifin Damfarar Wata Mata

 

Rundunar ‘yan sanda a ranar Juma’a ta gurfanar da wani mutum mai suna Oscar Akpan mai shekaru 30 a gaban wata kotun majistare ta Ajah bisa zargin damfarar wani mai siyan mota Naira miliyan 1,300,000.

Akpan, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume biyu da suka hada da samu ta hanyar karya da kuma sata, an ce ya arce da kudin.

An gurfanar da shi ne a gaban kotu bayan ‘yan sanda sun kama shi.

Dan sanda mai gabatar da kara, sufeto Chinedu Njoku, ya ce wanda ake kara ta hanyar damfara ne ta samu kudin daga hannun mai kara, Blessing Sunday, tare da alkawarin ba ta mota kirar Volkswagen T4.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Oktobar 2022, a Estate Jakande da ke yankin Lekki na jihar Legas.

A cewar sa, laifukan ana hukunta su ne a karkashin sashe na 314 da 287 na dokar laifuka ta jihar Legas 2015.

Sai dai wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ‘yan sanda suka cike takardar bincike akansa.

Sakamakon haka, Alkalin Kotun, O. M. Daramola, ya bayar da belinsa a kan kudi Naira 300,000, tare da wadanda za su tsaya masa har guda biyu.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa, Alkalin kotun ya dage sauraron karar har zuwa ranar 9 ga watan watan Junairun 2023, domin cigaba da shari’ar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet