Uncategorized
Ronaldo ya kulla kwantiragin shekaru 2 da Al Nassr ta Saudi Arabia
Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo ya amince da kulla kwantiragin shekaru 2 tsakaninsa da kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr da ke Saudi Arabia akan farashin da aka yi ittifakin ya kai yuro miliyan 200.
Tuni Ronaldo mai shekaru 37 ya sa hannu kan kwantiragin wanda zai kai shi daga yanzu zuwa shekarar 2025.
A kalamansa lokacin da ya ke sanya hannu kan kwantiragin, Ronaldo ya ce yana matukar farin cikin taka leda a wata gasa ta daban sabanin wadanda ya taka leda da su a baya.
Tuni dai Al Nassr ta wallafa hoton Ronaldon rike da rigar kungiyar mai dauke da lamba 7, lambar da dan wasan ke amfani da ita a duk kungiyar da zai takawa leda.
Tauraron na Portugal da ya raba gari da Manchester United a watan jiya bayan fuskantar takun saka da mai horarwa wanda ya kai shi ga furta wasu kalamai da suka fusata kungiyar, ya ce yana fatan bayar da gudunmawar da zai iya ga kungiyar ta Al Nassr.
Ronaldo wanda aka ga salon taka ledarsa a kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da Juventus da kuma Manchester United, kulla kwantiragin nasa da Al Nassr na zuwa bayan rashin tabuka abin kirkinsa a gasar cin kofin Duniya da ta gudana a Qatar.
Acewar Ronaldo a qage ya ke ya hadu da abokanan wasansa na kungiyar don fara taka leda.
Sau 9 kungiyar ta Al Nassr na lashe kofin lig din Saudi Arabia said ai rabonta da kofin tun shekarar 2019.
