Tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo, ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour Party LP, Peter Obi, a matsayin gwaninsa a zaɓen baɗi da ke ƙaratowa.
Obasanjo, ya bayyana hakan ne ta cikin saƙo sa na sabuwar shekara a yau Lahadi.
Ya ce, Peter Obi ya yi wa sauran ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen mai ƙaratowa fintinkau musamman ta fannin ilimi da ƙwarewa.