Connect with us

Labarai

Dubun Matashin Da Ya Dade Yana Satar Rufin Kwano Da Kofofin Masallachi Ta Cika

Wani matashi ya tafka wata gagarumar aika-aika inda ya shiga har cikin masallatai yayi zamba cikin aminci.

Matashin mai suna Abba Haruna ya shiga hannun ƴan sanda bayan ya sace rufi da ƙofofin masallatai 14 a cikin ƙananan hukumomi uku a jihar Jigawa, da sunan zai gina musu sababbi.

Matashin da ake zargin dai ya shiga hannu ne bayan an gano cewa ɗan damfara ne. Ya cire dukkanin rufi da ƙofofin masallatan sannan ya sayar da su ga ƴan bola-bola.

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa kakakin kotun majistare ta garin Kiyawa, Abbas Rufai Wangara, yace ana zargin Haruna da lalatawa haɗe da satar kwanon rufi, ƙofofi da tagogin masallatai.

Hakanan kuma BBC ta rahoto cewa wanda ake zargin yayi awon gaba da kayan masallatai 14 a ƙananan hukumomin Taura, Kiyawa da Jahun na jihar ta Jigawa.

Dagacin garin Kanoke, Ussaini Wanzam Ilyasu, ya gayawa ƴan jarida cewa Haruna ya zo ƙauyen na su wasu makonni da suka gabata, inda yace musu yana aiki da wata ƙungiyar larabawa mai zaman kanta wacce zata gina musu babban masallaci, domin haka sai su ruguza tsohon.

Haruna ya shiga hannu ne bayan an ganshi yana ƙoƙarin yaudarar wani ƙauyen inda jami’ai suka ankara bayan ganin alamun rashin gaskiya a tattare da shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet