Connect with us

Labarai

Yadda Wani Mai Yukurin Rabon Rigima Ya Kare Da Yanke Hannu A Kano

Wani matashi mai suna Salisu Hussaini bai da tunanin cewa kasancewarsa mai son zaman lafiya da raba fada tsakanin wasu makwabtansa biyu a Kano zai canza rayuwarsa ta hanyar da bai taba tunani ba.

Lamarin da ya faru a unguwar Fagge da ke cikin birnin Kano, ya sa Hussaini, mai shekaru 21 tela ya rasa hannunsa bayan wani fusatacce mai suna Abubakar Ayuba, wanda aka fi sani da Namama ya caka masa wuka.

City & Crime ta tattaro cewa Namama da wani Abdullahi Muhammad wanda aka fi sani da Alhaji Ozil, sun fafata fada ne a ranar 30 ga watan Maris, wanda ya rikide zuwa mummunan tashin hankali lokacin da Hussaini ya yanke shawarar shiga tsakani tare da samar da daidaito, amma sai aka yi masa wuka da ya kai ga harbuwa ga kamuwa da cuta.

Da yake ba da labarin abin da ya faru a kan gadon jinya inda aka ake masa hannu na dama, Hussaini ya yi kira ga hukumomi da su kwatar masa hakkinsa saboda ba zai iya tunanin rayuwa ba tare da hannu ba.

Ya ce, “Lokacin da na ga suna fada suna barazanar kashe kansu, sai na yanke shawarar shiga tsakani domin a samu zaman lafiya. Na tunkari Namama wanda na san yana da matsala, na ba shi shawarar ya daina barazanar kashe mutane. Ya fito da wuka yana kokarin soka min a cikina, amma da na zare sai ya cake ni a hannu.

“Sai aka kai ni asibiti inda suka bukaci dan sanda ya zo. Bayan an gama jinyar hannuna bai gyaru ba. Daga nan sai na koma asibitin kwararru na Murtala Muhammed inda suka kai ni asibitin koyarwa na Jami’ar Aminu Kano (AKUTH) daga baya kuma zuwa nan (Asibitin kashi na Dala) inda suka tabbatar da cewa hannun ya rube kuma dole a yanke.”

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce wanda ake zargin yana hannunsu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet