Kasuwanci
‘Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Karancin Sabbin Kudin Naira
Kwanaki 17 bayan fitar da sabon takardun kudi na N200, N500 da N1,000 da Babban Bankin Najeriya CBN ya yi, miliyoyin ‘yan Najeriya ba su gani ko yin kasuwanci da takardun ba.
Da yawan wadanda suka zanta da Jaridar Daily Trust a Abuja, Kano da Legas na nuna damuwa kan karancin kudin da ake samu, musamman a Na’urar ATM na bankuna.
Wannan damuwar ta sabbin takardun kudin Naira na zuwa ne kasa da kwanaki 28 zuwa wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da CBN ya kayyade na cire tsofaffin takardun kudin Naira.
Babban bankin na CBN ya gabatar da sabbin takardun kudin ne a ranar 15 ga watan Disamba, 2022, inda ya ce yana daga cikin matakan shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, karkatar da kudaden waje da tsarin banki, yaki da cin hanci da rashawa da kuma hana biyan makudan kudade ga masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da sauransu.
Binciken da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna cewa, kwastomomin da suka ziyarci gidajen banki kafin hutun, sun kuma bayyana cewa an ba su tsofaffin takardun kudaden ne.
An samu labari daga wasu ma’aikatan banki a Ojo, Ikeja da Agbara a jihohin Legas da Ogun cewa ba a ba su sabbin takardun kudi ba yayin da wasu ke cewa CBN na raba sabbin takardun kudin
An kuma ruwaito cewa yawancin kwastomomin da suka biya da tsabar kudi a manyan kantuna da shaguna a lokacin bukukuwan suna amfani da tsofaffin takardun kudin ne.
