Connect with us

Labarai

Hukumar INEC Za Ta Fara Raba Katin Zabe A Yankuna Da Mazabu Ranar Juma’a

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa ta ce za ta fara raba katinan zabe na dindindin ga wadanda suka cancanta, daga ranar Juma’a 6 ga watan Janairu zuwa Lahadi 15 ga watan Janairun 2023.

Festus Okoye, kwamishinan kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a ne ya bayyana hakan a daren ranar Alhamis a wata sanarwa.

Okoye ya tunatar da cewa an yanke shawarar karkatar da tarin kayan zabe a yankunan rajista da Masu rajista a wani taron koli da aka gudanar a watan Disambar da ya gabata a Legas, tare da dukkan sakatarorin gudanarwa da kwamishinonin zabe (RECs) daga jihohi 36 na Tarayyar Najeriya da kuma babban birnin tarayya yana halarta.

Kwamishinan INEC na kasa a cikin sanarwar ya bukaci duk wadanda suka yi rajistar zabe wadanda har yanzu ba su karbi katin zaben ba da su yi amfani da damar da aka baiwa mazabun da su zo su karba.

Bayan ranar 15 ga watan Janairun 2023, aikin zai koma ma’aikatun kananan hukumomin hukumar har zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2023. Duk masu rajista da cancantar suna iya karbar katin zabe daga karfe 9:00 na safe zuwa karfe 3:00 na rana, har da ranakun Asabar da Lahadi.

Jaridar Alkiblah ta rawaito Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Duk wadanda suka nemi a maye gurbin katin zaben da suka bata, ko suka lalace ko suka bata, za su iya karbar katinsu a mazabu wajen rijistar a wannan lokaci, haka kuma ya shafi wadanda suka yi rajista kafin zaben 2019. kuma har yanzu ba su karbi katunan su ba.

“katin zaben na wadanda suka nemi canja wurin suna nan a karba a kananan hukumomi da wuraren rijista da suke da niyyar kada kuri’a ba a jiha ko karamar hukumar da suka yi canjin ba.

“Hukumar ta yaba da hakuri da fahimtar ’yan Najeriya da suka je ofisoshin kananan hukumomin mu daban-daban domin karbar katin zaben. A wajen samar da katunan don karba, hukumar na kuma kokarin ganin cewa tsarin ya yi sauki kuma babu cikas ga ‘yan Najeriya.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet