Labarai
Jihar Borno Ta Sami Zaman Lafiya Da Tsaro Kashi 90 Cikin 100 Kafin Zabe – Zulum
Gwamna Babagana Zulum ya ce jihar Borno tana da kashi 90 cikin 100 na tsaro da kwanciyar hankali gabanin babban zabe na 2023.
Ya bayyana haka ne a yau Juma’a bayan ziyarar ban girma da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Gwamnan ya baiwa al’ummar da suke kada kuri’a tabbacin kare lafiyar su kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.
Harin da aka kai kan tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a ranar 22 ga watan Nuwamba a Maiduguri, babban birnin jihar, ya kara jawo hankalin jami’an tsaro game da yiwuwar tashin hankali gabanin zaben.
Da aka tambaye shi ko me yake yi domin tabbatar wa wadanda ba su damu da karbar katin zabe ba saboda fargabar rashin tsaro ba za su iya amfani da shi a lokacin zaben ba, sai ya ce: “Al’ummar Jihar Borno sun kada kuri’a a zaben 2015. Sun kuma kada kuri’a a zaben 2019. Shin za ku iya kwatanta yanayin tsaro a 2019 da 2015 da kuma yanzu? Yanayin tsaro ya inganta sosai sama da kashi 90, don haka ba mu da wata matsala.
“Masu cancanta za su iya zuwa su kada kuri’unsu a ranar zabe, Insha Allahu a Jihar Borno, ba mu da wata matsala.”
Zulum, yayin da yake mayar da martani ga wata tambaya kan yanayin tsaro a jiharsa, ya ce: “Mun gode da cewa an samu ci gaba sosai ta fuskar tsaro a jihar Borno.
“Muna kan aiki sosai a yanzu, gyaran da kuma sake tsugunar da jama’a yana tafiya yadda ya kamata. Muna sa ran ganin yadda za mu gyara hanyar Maiduguri, Gamborun-Gala sai kuma titin Maiduguri zuwa Banke da nufin bude wa jama’a damammaki don samun abin dogaro da kai,” inji shi.
