Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alfred Alabo ya fitar.
Sanarwar ta ce, wasu ƴan bindiga uku da ba a san ko su wanene ba, a cikin wata mota ƙirar CR-V Jeep mai launin ruwan toka, sun kutsa kai gidan shugaban majalisar wanda yake a rukunin gidajen tarayya a karamar hukumar Jos ta Kudu. ranar Alhamis.
Mai magana da yawun rundunar, ya kuma bayyana cewa, bayan sun bi sawun shugaban majalisar zuwa gidansa, masu garkuwar sun yi yunƙurin shiga gidan domin yin garkuwa da shi, sai dai hakan ba ta samu ba sakamakon ƙoƙarin ƴan sandan da ke aikin gadi a gidan da suka fatattaki ɓata garin.
Haka kuma ya ƙara da cewa, rundunar ƴan sandan tana ci gaba da ƙoƙarin zaƙulo wadanda ake zargin tare da gurfanar da su a gaban Kotu.
