Connect with us

Uncategorized

Al Nassr ta kori daya daga cikin ‘yan wasanta saboda Ronaldo

Cristiano Ronaldo zai iya buga wasansa na farko a gasar kwallon kafar kasar Saudiyya a ranar 22 ga watan Janairu, bayan da kungiyarsa Al Nassr ta samu damar yi masa rijista, kamar yadda wata majiya ta kulob din ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Da fari dai har zuwa lokacin da ta gabatar da Ronaldo ga magoya bayanta a makon jiya, Al Nassr ba ta yi wa sabon dan wasan na ta rijista ba, saboda cikewar guraben da take shi na ‘yan wasa 8 da take da damar dauka daga kasashen ketare.

Daga bisani Ronaldo ya samu damar shiga cikin tawagar ta Al Nassr bayan da kungiyar ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninta da dan wasan kasar Kamaru Vincent Aboubakar.

A halin yanzu Cristiano zai samu buga wasan da kungiyar za ta kara da Ettifaq a ranar 22 ga watan Janairu, idan ya kammala mutunta hukuncin dakatarwar wasanni biyu da hukumar kwallon kafar Ingila ta yi masa a watan Nuwamba, saboda fasa wayar wani mai goyon bayan Everton da ya yi a lokacin da yake buga wasa a Manchester United cikin watan Afrilun 2022.

A bangaren Vincent Aboubakar kuwa, jim kadan bayan soke kwangilarsa da Al Nassr ta yi, sai ya bayyana cewar ya dade yana tunanin cewa Messi ya yi wa Ronaldo zarra a fagen kwallon kafa, kuma bayan atsayen da yayi tare da Cristiano, sai ya fahimci cewar lallai bai yi kuskure a tunanin na sa ba.

Akwai dai wasu majiyoyi da suka ruwaito cewar Jami’in mai yiwuwa Vincent Aboubakar mai shekaru 30 ya koma taka leda a Manchester United, wadda har yanzu ba ta maye gurbin da Cristiano Ronaldo ya bari ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet