Labarai
Tsohon Mai Taimakawa Ganduje Na Musamman Ya Fice Daga Jam’iyyar APC
Tsohon babban mataimaki na musamman ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Alhaji Sani Mohammed, wanda aka fi sani da Sani Rogo ya fice daga jam’iyyar APC.
Mohammed ya mika takardar ficewar tasa ne daga jam’iyyar, a wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar, a Unguwa Uku Cikin Gari, da ke karamar hukumar Taruani, mai kwanan wata 9 ga watan Janairun 2023.
SOLACEBASE ta ruwaito a ranar Juma’ar da ta gabata, Sani Mohammed ya yi murabus a matsayin babban mataimaki na musamman ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
“Ina ci gaba da godiya ga damar da dangantakar da ta samo asali daga zama memba na jam’iyyar,” in ji wasikar.
Majiyoyi sun shaida wa SOLACEBASE cewa fitaccen dan siyasar nan, Sani Rogo da ke karamar hukumar Tarauni ya fice daga jam’iyyar ne bisa rashin adalcin da ake nuna masa a jam’iyyar.
